Muslim Library

Surah Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud)

Select reciter

Hausa

Surah Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya count 36
Facebook Twitter Google+ Pinterest Reddit StumbleUpon Linkedin Tumblr Google Bookmarks Email
وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ ( 1 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 1
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُوا عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ ( 2 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 2
Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ ( 3 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 3
Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
أَلَا يَظُنُّ أُولَٰئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ ( 4 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 4
Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
لِيَوْمٍ عَظِيمٍ ( 5 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 5
Domin yini mai girma.
يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ ( 6 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 6
Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ ( 7 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 7
Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌ ( 8 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 8
Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ ( 9 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 9
Wani 1ittãfi ne rubũtacce.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ ( 10 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 10
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ ( 11 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 11
Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ ( 12 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 12
Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ ( 13 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 13
Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
كَلَّا ۖ بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ ( 14 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 14
A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
كَلَّا إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ ( 15 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 15
A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُو الْجَحِيمِ ( 16 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 16
Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ ( 17 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 17
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ ( 18 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 18
A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَ ( 19 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 19
Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ ( 20 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 20
Wani littãfi ne rubũtacce.
يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَ ( 21 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 21
Muƙarrabai suke halarta shi.
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ ( 22 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 22
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ ( 23 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 23
A kan karagu, suna ta kallo.
تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِ ( 24 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 24
Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ ( 25 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 25
Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
خِتَامُهُ مِسْكٌ ۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ ( 26 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 26
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
وَمِزَاجُهُ مِن تَسْنِيمٍ ( 27 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 27
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ ( 28 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 28
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُوا مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَ ( 29 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 29
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
وَإِذَا مَرُّوا بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ ( 30 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 30
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
وَإِذَا انقَلَبُوا إِلَىٰ أَهْلِهِمُ انقَلَبُوا فَكِهِينَ ( 31 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 31
Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَضَالُّونَ ( 32 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 32
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ ( 33 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 33
Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُوا مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ ( 34 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 34
To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ ( 35 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 35
A kan karagu, suna ta kallo.
هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ ( 36 ) Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 36
Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?
Facebook Twitter Google+ Pinterest Reddit StumbleUpon Linkedin Tumblr Google Bookmarks Email

Select language

Select surah